Holocaust: Shekaru 75 da aikata kisan kiyashi
January 23, 2020Talla
Taron na wannan Alhamis ya gudana ne a cibiyar tunawa da ta'asar ta Yad Vashem da ke a Isra'ila, shugabanni da 'yan siyasa daga kasashe kimanin 40 ne suka tattauna matakan yaki da kyamar Yahudawa.
Yawan kai hare-haren kan Yahudawa dai ba bakon abu ba ne a kasashen da dama na duniya, ciki har da nan Jamus, ko a karshen shekarar da ta gabata a birnin Freiburg an kai hari kan wani matashi Bayahude dan shekara 19 da haihuwa guda ne a cikin dubban take-taken kyamar Yahudawa da ake samu a kowace shekara a Jamus.