1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakar cin hanci ta rediyo a Laberiya

March 15, 2017

Kungiyar da ke yaki da cin hanci ta duniya wato Transparency International ta ce kasar na lamba ta 94 daga kasashe 179 masu matsalar cin hanci a duniya.

https://p.dw.com/p/2ZCJe
DW Sendung Africa on the Move
Hoto: DW

Jonathan Domah a wani shiri a tasahr Radio Maria ya bayyana manufofinsu na yaki da cin hanci da rashawa inda kuma ya bankado wata cuwa-cuwa ce a harkar ilimin kasar. Jonathan na zargi wasu malamai da kwasar kudaden da ake warewa sayen kayan koyo da koyarwa ne. Ya yaba tasirin da rediyo ke yi wajen bayyana mutanen da aka samu da rikicin cin hanci:

"Ya na da muhimmaci saboda al’umma ta dogara ne kanmu matasa matuka. Ana girmama abin da muke yi sosai. Don haka muke kokarin sanar da sakamakon duk wani abin da muka bankado musamman binciken da muke ga kowa." 

Bayan sauraren kusan batun wasu malamai takwas da aka samu da debe kudaden makarantu, wasu mazauna Monrovia sun bayyana ra’ayoyi kamar haka:

"Mu ne talakawa, ya kamata mu amfana daga dukiyar kasarmu. Duba duk arzikin da kasar nan ke da shi, ba wani abin da mu talakawan mu ke samu."

"Babbar matsala ce rashawa a kasar nan. Kowane bangare akwai shi. Da gwamnatin da ma bagarori masu zaman kansu."

Jonathan Domah mai fafutukar yaki da rashawa a Liberian ya ce kusan kullum sai sun sami koke daga jama’a don haka ta hanyar amfani da radiyon nan, suna aika wa jama’a sako ne cewar wannan aiki ne da ke wuyan kowane dan kasa, ga duk mai kyamar rashawa ta faro daga kan shi.