Yake-yake sun haifar da karuwar 'yan gudun hijira
June 20, 2017Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nunar da cewa mutane miliyan 65 da dubu 600 ne ke gudun hijira a sassan duniya daban-daban. Wannan adadi dai ya zarta yawan 'yan gudun hijira na shekara da ta gabata da wanda aka kiyasta yawansu kan abin da bai zarta dubu 300 ba.
Wannan lamarin dai na nuna cewar kowane mutum daya cikin mutane 113 na duniya ya kaurace wa muhallinsa a halin yanzu saboda dalilai daban-daban musamman ma dai yake-yake. Kasashen Syriya da Iraki da Kolombiya na sahun farko na wuraren da aka fi samun 'yan gudun hijira wanda akasarinsu mata ne da yara kanana.
Duk da alkawuran da kasashe duniya suka yi a taron da aka gudanar a watan Afirilu a birnin Brussels na kasar Beljiyam, har yanzu hukumar kula da 'yan gudun hijira na ci gaba da mika kokon bararta ga kasashe masu hannu da shuni kan a dafa mata wajen tallafawa wanda wannan matsala ta shafa.
Mafi akasarin 'yan gudun hijira dai sun fito ne daga kasashe 'yan Rabbana ka wadatamu ciki kuwa har da Sudan ta Kudu da Tarayyar Najeriya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wadanda ke fama da rikice-rikice. Galibin mutanen da suka fito daga wadannan kasashe kan ratsa teku don shiga nahiyar Turai da nufin samun ingantaciyyar rayuwa wanda da dama daga cikinsu kan rasa rayukansu yayin wannan yunkuri.