Fargaban MDD a kan yakin Sudan
May 23, 2023Talla
Manzon musammum na MDD a Sudan Volker Perthes ya shaida wa kwamitin sulhu na MDD cewar yana da fargabar kan yakin da ake yi a Sudan ya rikide ya koma na kabilanci. Volker ya ce a wasu sassan kasar, yakin da ake yi tsakanin sojojin ya sake farfado da rikicin kabilanci tsakanin al'umomin.Tun a ranar 15 ga watan Afrilu, yakin da ake gwabza tsakanin sojojin Janar Abdel Fattah al-Burhane da na dakarun rundunar daukin ggagawa ta FSR na Janar Mohamed Hamdane Daglo ya yi sanadin mutuwar duban rayuka tare da raba sama da miliyan guda da muhallansu.