Yamen: Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki
April 2, 2022Talla
Yarjejeniyar da aka cimma karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya za ta shafe tsawon watanni biyu ne a kasar da yaki ya daidaita, kana kuma tuni ta soma aiki wannan Asabar daya ga watan Ramadana.
Bangarorin biyu da suka aminta da tsagaita buda wuta, sun kuma yi na'am da zirga-zirgar jirage daga wasu yankuna zuwa babban birnin kasar Yamen Sanaa, baya ga bude mashigar ruwa ta Hodeida da ke yammacin kasar ga tankokin dakon danyen mai, a cewar manzo na musamman na MDD da ya shiga tsakani Hans Grundberg.