Yamutsi ya barke a birnin Tripolin Libiya
January 15, 2018Tun da sanyin safiya aka fara jin harbe harbe na tashi wanda ya yi sanadiyyar rufe filin jirgin saman Mitiga har sai abinda hali yayi.
Rundunar tsaro ta Rada wacce ke yaki da ta'addanci da kuma muggan laifuka a kasar ta bayyana cewar ta na ci gaba da samun hari daga Kungiyoyi daban daban da ta kame mambobinsu ta kuma tsare su sakamakon zarginsu da tada zaune tsaye a fadin kasar.
Rundunar ta kara da cewar an kai wannan hari ne da niyyar fidda wasu 'yan kungiyar ta'addanci ta IS dake tsare a gidan yarin.
A halin yanzu gawarwaki 10 na fursunonin da akayi yunkurin kubutarwa na ajiye a wani asibiti da ke kusa da gidan yarin kamar yadda ma'aikatar lafiyar kasar ta sanar. Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da kokarin ganin an yi zabe a kasar ta Libiya kafin karshen wannan shekarar wanda ta ke fatan zai daidaita al'amura a kasar mai arzikin mai.