'Yan adawa na son ture Netaanyahu
May 31, 2021Talla
A kasar Isra'ila shugaban karamar jam'iyya mai ra'ayin rikau, Naftali Bennett ya nuna aniyar kafa wata gwamnatin hadin kan kasa da 'yan adawa da Firaminista Benjamin Netanyahu, a wani gagarumin mataki da ke da burin kawo karshen mulkin shekaru 12 na shugaban Isra'ilan.
Sai dai Netanyahu ya gargadi 'yan jam'iyyarsa su guji ba wa 'yan adawa damar kafa sabuwar gwamnati da Naftali Benett ke shirin jagoranta, Netanyahu dai na fuskantar matsin lamba kan tuhumar cin hanci da rashawa.