'Yan adawa sun yi gangami a Kenya
October 6, 2017Talla
A biranen Nairobi da Mombasa ma an gudanar da gangamin, sai da masu aiko da rahotanni sun ce jama'a da dama ba su fito ba. Bayan soke zaben kasar na Kenya da kotun ta yi a cikin watan Augusta da ya gabata 'yan adawar kasar sun kaddamar da wani kampe na nuna adawa da hukumar zaben wacce za ta shirya sabbin zabubukan da za a gudanar a ranar 26 ga wanan wata na Oktoba saboda abin da suka kira rashin adalcin manbobin hukumar.