Rashin tabbas kan zaben shugaban kasar Tanzaniya
October 28, 2015'Yan adawa a Tanzaniya sun yi kira da a soke zaben shugaban kasar da aka yi ranar Lahadi da ta gabata. Dan takarar neman shugabancin kasar na kawancen jam'iyyun adawa Edward Lowassa ya fada a birnin Dar es Salam cewa sakamakon zaben da aka bayar yanzu na cike da kura-kurai da arangizon kuri'u saboda haka ba su da madogara. Da farko dai hukumar zaben tsibirin Zanzibar da ke cikin hadaddiyar Jamhuriyar Tanzaniya, ta soke zaben shugaban kasa saboda kura-kurai da ta ce an tabka. Shugabann hukumar zaben ya ce yawan kuri'un da aka tattara a wasu mazabu sun fi yawan mutanen aka yi rajista. Jagoran adawa a Zanzibar wanda tun a ranar Litinin ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben, Ma'alim Seif Hamad na jam'iyyar CUF, ya yi tir da wannan mataki da ya ce yunkuri ne na hana shi rike madafun iko. An hana wasu wakilan tawagogin sa ido a zabe shaida yadda ake kidayar kuri'un.