1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan awaren Kamaru sun bijire wa sulhu

Abdullahi Tanko Bala
September 30, 2019

'Yan awaren Kamaru da ke yankin da ke magana da Turancin Ingilishi, sun kaurace wa tattaunawar da hukumomi suka fara a wannan Litinin, inda suka sha alwashin ci gaba da tayar da kayar baya.

https://p.dw.com/p/3QT5g
Kamerun Wahlen
Hoto: Dirke Köpp

Shugaba Paul Biya na Kamarun ne dai ya shirya zaman neman sulhu tsakanin gwamnati da 'yan awaren, a kokarin ganin an kawo karshen rikicin da kasar ke ciki shekaru biyu yanzu.

Su dai mazauna bangaren na Ingilishi, na zargin nuna musu wariya ne da bangaren kasar mai rinjaye na Faransanci ke yi.

A baya gwamnatin kasar ta sha afka wa mutanen da a farko suka ce suna zanga-zangar lumana, wadanda suka hada da malaman makarantu da kuma lauyoyi.

Sama da mutum dubu uku ne dai suka salwanta a rikicin na Kamaru, wasu fiye da dubu 500 kuwa suka rasa matsugunai.

Kasar dai na da gundumomi goma wadanda biyu daga cikin su da suka hada da yankin arewa maso yamma mai hedikwata a Bamenda da kuma Kudu maso yamma mai hedikwata a Buea ke magana harshen Turanci