Daruruwan ‘yan bindiga na yawo da makamai a Najeriya
April 1, 2022Yanayi ne dai da ake bayyana shi a matsayin ‘yan bindigar dajin na watan-gaririya a jihohin da rashin tsaro ya kara kamari da kazanta domin kuwa a gungu da suka zarta 200 zuwa 300 ne aka gansu suna kai hare-hare a kan jama’a a wadannan jihohi.
‘Yan bindigar sun kai hare-hare munana tare da garkuwa da jama’a a gefen Abuja irin karamar hukumar Kwali da kauyen Rubochi baya ga wanda suka yi a Kaduna da jihar Neja.
‘’Dama ‘yan bindigar nan, ni na sha fadin suna yawo a cikin kauyuka a gungunsu fiye da 1000” Masanin tsaro da bayanan sirri Dakta Yahuza Getso ya shaida wa DW.
Rahotanni sun bayyana wata arangama da ‘yan bindigar dajin suka yi da sojoji a kusa da Suleja a ranar Alhamis ta yi muni, inda ake fargabar an kashe sama da sojoji tara tare da raunata wasu. Duk da ana yada hotunan bidiyo na wannan hari, sojojin Najeriya sun ki tabbatar da labarin kai wannan hari. Sai dai tuni ‘yan majalisar dokokin kasar suka bayyana cewa tura fa ta kai bango. Shin abin yafi karfin gwamnatin ne ko kuwa mene ne? Hon Aminu Suleiman dan majalisar wakilan Najeriyaer ne. Ya shaida wa DW cewa “Masifar ta kai ga cewa tsaro ya lalace duk da kudaden da muke amince wa gwamnati ta kashe a kan tsaro. Mun rasa abin da ke faruwa.”
Tuni dai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake bai wa manyan hafsoshin tsaron kasar umurnin su kawo karshen lamarin. To sai dai bazuwa da ma kazantar al’amarin da ya kawo ga Abuja shelkwatar Najeriya, na jefa tambayoyi. Major Yahya Shunku masani ne a fanin tsaro a Najeriya ya shaida wa DW cewa gwamnati ba ta dauki abin da gaske ba.