1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun sace sarkin Kajuru

Binta Aliyu Zurmi MAB
July 11, 2021

Masu satar mutane sun yi awon gaba da sarkin Kajuru da iyalansa 12 a jihar Kaduna ta tarayyar Najeriya. Ya zuwa wannan lokacin dai masu aiko da rahotanni sun ce maharan ba su kira ba balle a ji bukatarsu ko dalilinsu.

https://p.dw.com/p/3wKrc
Karte Nigeria englisch

Masu satar mutane sun yi awon gaba da sarkin Kajuru da iyalansa 12 a jihar Kaduna da ke arewacin taryyar Najeriya. Rahotanni na cewar maharan sun isa fadar ta sarkin Kajuru Alhassan Adamu mai shekaru 83 kuma suka sace shi da matansa da kuma kananan yara. A cewar jikan basaraken da ya sha da kyar, 'yan bindigan sun isa fadar ne da misali 12:30 na rana.

Wata majiya daga fadar ta kajuru ta ce sarkin ya san da shirin da ake yi na sace shi, don ko a jiya ya yi wata ganawa ta gaggawa da jami'an tsaro inda ya sanar da su halin da ake ciki. Sai dai duk da hakan bai hana maharan  kaddamar da shirinsu ba.

Har ya zuwa wannan lokacin dai masu aiko da rahotanni sun ce maharan ba su kira ba balle a ji bukatarsu. Jihar Kaduna dai a 'yan watannin nan na fuskantar barazanar sace mutane domin neman kudin fansa, lamarin da gwamnatin jihar ta ce ba za ta lamunta ba, amma kuma ta kasa magance matsalar.