1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijiara na komawa gida a Najeriya

Yusuf BalaDecember 17, 2015

A cewar Sani Datti da ke magana da yawun hukumar NEMA tsakanin ranakun Litinin zuwa Larabar jiyar 15.12.2015 akwai 'yan Najeriya 1,187 da suka koma daga kasar Kamaru.

https://p.dw.com/p/1HOto
Nigeria Flüchtlingskamp Yola
'Yan gudun hijira a kan hanyarsu ta komawa gida cikin rashin tabbasHoto: picture alliance/dpa

Fiye da 'yan gudun hijira 1000 ne da ke gudun tsira da rai a makwabtan kasashe sakamakon ayyukan mayakan Boko Haram suka koma gida Najeriya a cikin wannan mako kamar yadda hukumar agajin gaggawa ta kasa a Najeriyar NEMA ta bayyana a ranar Laraba. A cewar Sani Datti da ke magana da yawun hukumar tsakanin ranakun Litinin zuwa Larabar 15.12.2015, akwai 'yan Najeriya 1,187 da ke neman mafaka bayan tsallaka iyaka da Kamaru, yanzu sun koma sansani da aka tanadar musu a jihar Adamawa Arewa maso Gabshin kasar.

Cikin sirri dai Amirka na tura dakarunta zuwa Yammacin na Afirka a yaki da mayakan na Boko Haram masu ikirarin mubayi'a da kungiyar IS dan tallafawa dakarun kasar Kamaru a kan iyaka da Najeriya. Kaftin Victor Guzman na daga cikin wadannan dakaru ya kuma yi karin bayani kamar haka.

"Amirka na bada bayanai nasirri ga dakarun, da kayan da zasu yi aiki dan murkushe wadannan 'yan ta'adda da ke barazana ga yankunansu kai har ma da sauran kasashe".

A cewar hukumar ta NEMA dai a Najeriya cikin makwanni da ke tafe ana sa ran 'yan gudun hijira 15,000 zasu koma gida.