1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

'Yan gudun hijira na komawa Siriya

Suleiman Babayo AMA
December 17, 2024

Sakamakon faduwar gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad na Siriya kimanin 'yan kasar kimanin milyan guda za su koma kasarsu zuwa tsakiyar shekara mai zuwa ta 2025, mutanen da suka stere sakamakon yakin basasa.

https://p.dw.com/p/4oG64
'Yan Siriya
'Yan SiriyaHoto: Amr Abdallah Dalsh/REUTERS

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa kimanin 'yan kasar Siriya kimanin milyan guda za su koma kasarsu zuwa tsakiyar shekara mai zuwa ta 2025, wannan bayan faduwar gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce faduwar tsohuwar gwamnati ya janyo komawar 'yan gudun hijira.

Karin Bayani: Ina makomar Siriya bayan kifar da gwamnati?

Ita ma kungiyar Tarayyara Turai ta bayyana shirin sake bude ofishinta da ke birnin Damuscus fadar gwamnatin kasar ta Siriya. Shugabar hukumar ta Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta bayyana kara kudin taimakon 'yan gudun hijira da ake bai wa kasar Turkiyya da kimanin dala milyan dubu.

A karon farko cikin shekaru 12 an bude ofishin jakadancin Faransa da ke birnin Damascus na kasar Siriya. Ita dai Faransa ta rufe ofishin jakadancin sakamakon yakin basasa da kasar Siriya ta samu kanta a ciki. A shekara ta 2012 Faransa ta yanke hulda da gwamnatin tsohon Shugaba Bashar al-Assad.