1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira sun fuskanci hari a Nijar

Salissou BoukariJune 17, 2016

Da yammacin ranar Alhamis ce wasu mutane suka kai hari a sansanin 'yan gudun hijira na Nguagam da ke Arewacin birnin Diffa a Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/1J8W8
Niger Bevölkerungswachstum Frau mit Kindern
Wasu 'yan gudun hijira a jihar DiffaHoto: Getty Images/AFP/O. Omirin

Harin ya wakana ne jim kadan bayan da wata tawaga da ministan tsaron cikin gidan kasar ta Nijar Mohamed Bazoum ke jagoranta, ta kai ziyara a wannan sansani da ke kumshe da dubban jama'a.

Ministan tsaron cikin gidan na Nijar da ya tabbatar da wannan labari, ya ce ya zuwa wannan lokaci dai ba su da adadin mutanen da suka rasu ko suka jikkata ya yin wannan hari. A ranar uku ga watan nan ne dai na Yuni 'yan Boko Haram suka kai hari a garin Bosso tare da hallaka sojoji 26 da kuma jikkata wasu fiye da 100, wanda hakan ya haddasa tserewar jama'a daga garin na Bosso da ma wasu garuruwa na yankin domin neman mafaka.

Sai dai rahotanni na cewa, 'yan Boko Haram din da dama sun shiga kuma sun sun sade cikin 'yan gudun hijiran abun da ke zama babban kalubale.