1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijirar Sudan ta Kudu cikin ƙangi

August 8, 2014

Kimanin mutane dubu 75 suka ƙaurace wa yaƙin da ake yi sa Sudan ta Kudu zuwa Yuganda, galibi yara ƙanana waɗanda ke fuskantar ƙalubale na rashin samun ilimi.

https://p.dw.com/p/1CrYO
Südsudan Flüchtlinge an der Grenze zu Uganda
Hoto: DW/S. Schlindwein

Tun lokacin da yaƙi ya ɓarke a cikin watan Disamba na shekarar ta 2013 tsakanin dakarun gwamnati Sudan ta Kudun da na 'yan tawayen. Jama'a da dama wasu a ƙasa wasu cikin motoci shaƙe suke ficewa daga ƙasar zuwa Yuganda, waɗanda sassanin 'yan guhun hijira na Nyumanzi da ke kan iyaka da Sudan ta Kudun ke karɓarsu.

A kowacce rana mutane dubu suke ficewa daga Sudan ta Kudu zuwa Yuganda

A wata ƙidiga da Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta bayyana a cikin watan Afrilun da ya gabata, ta ce a kowacce rana mutane kamar dubu suke ficewa daga ƙasar zuwa Yuganda. Fred Okapa wani jami'in Ƙungiyar World Vision ya ce suna da fargaba game da yadda kishi 65 cikin ɗari na 'yan gudun hijirar yara ne.

Südsudan Flüchtlinge an der Grenze zu Uganda
Hoto: DW/S. Schlindwein

''Babban ƙalubale shi ne maganar samar da ilimi ga yaran galibi waɗanda suka fito daga yankin gabashin Sudan ta Kudun suke zaune a cikin sassanin 'yan gudun hijirar. Galibinsu shekaru huɗu zuwa bakwai suke da shi, kuma makarantun da ke da akwai a nan, sun cikka maƙil ba sa iya ɗaukar sabbin 'yan makaranta''

Babu Tabbas a kan komawar 'yan gudun hijirar na Sudan ta Kudu zuwa gida

Da dama daga cikin 'yan gudun hijrar na Sudan ta Kudu da ke zaune a Yuganda sun yi tsamanin tashin hankalin da ake yi a ƙasarsu ba zai ɗauki lokaci ba mai tsawo, domin su samu damar komawa ƙasarsu. Sai dai a yanzu babu wani daga cikinsu wanda ya san lokacin da zai koma gida sakamakon yadda har yanzu aka gaza cimma wani shirin sassantawa tsakanin gwamnatin da 'yan tawayen.

Konflikt im Südsudan Flüchtlinge 17.01.2014
Hoto: Reuters

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal