1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan hamayya a Turkiyya sun bijire wa sakamakon zabe

April 17, 2017

Zaben raba gardamar Turkiyya ta raba kan al'umar kasar bayan fitowar sakamako a wannan Litinin. Bangaren masu adawa ya ce zai kalubalanci sakamakon da ya bai wa shugaba Erdogan nasara.

https://p.dw.com/p/2bLUw
Türkei Referendum Wahllokal in Diyarbakır
Hoto: picture alliance/AP Photo/E. Tazegul

Shugaban kasar Turkiyya Rejap Tayyip Erdogan ya lashe zaben raba gardamar kasar mai tarihi, zaben kuma da zai fadada karfin iko da yake da shi. Jamiyyun adawar kasar dai sun ce basu amince ba, a don haka ne suke cewa za su kalubalanci sakamakon zaben na jiya Lahadi.

Kasashen duniya na kiran yin taka tsantsan da zaben na Turkiyya, da shugaba Erdogan din ya sha da kyar. Wasu manyan kungiyar tarayyar Turai ma dai sun ce suna kallon lamarin cikin tsanaki.

Wani sakon hadin guiwa daga shugaban kugiyar ta EU John Claude Juncker da mai kula da dangantakar kasashe Federica Mogherini da ma Johannes Hahn ya ce suna dakon nazarin masu sa ido na kasashen duniya kan sakamakon wannan zaben da ke da 'yar karamar rata. Faraiminista Erdogan dai ya bijirewa kungiyar ta EU cikin shekarun da suka gabata.