1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan jihadi sun hallaka sojojin kasar Mali

Salissou Boukari
July 13, 2017

Rundunar sojojin kasar Mali ta sanar da mutuwar sojojinta guda uku, da kuma bacewar wasu guda biyar a yankin arewacin kasar. Mayakan jihadi ne dai suka kai musu hari a tsakanin birnin Gao da Menaka.

https://p.dw.com/p/2gTtR
Mali Soldaten
Sojojin kasar Mali masu sintiri a yankin arewacin kasarHoto: Getty Images/AFP/J. Saget

Rahotanni daga Bamako babban birnin kasar Mali na cewa akalla sojojin kasar uku ne suka mutu yayin da wasu guda biyar ba'a kai ga gano inda suke ba har ya zuwa ranar Alhamis 13 ga watan Yuli, bayan wani kwanton bauna da mayakan jihadi da ke yankin arewacin kasar suka ka yi musu. Sai dai kuma rundunar sojojin kasar ta Mali cikin wata sanarwa, ta ce ta kashe 'yan ta'addan 12  tare da kama daya daga cikinsu.

Sanarwar ta ce hari na baya-bayan nan da 'yan ta'addan arewacin kasar ta Mali suka kai wa sojojin a tsakanin birnin Gao da Menaka da ke arewa maso gabashin kasar, wanda da farko aka ce sojojin kasar ta Mali 10 sun bace, yanzu ta tabbata cewa sojoji uku sun mutu sannan wasu guda biyar sun bace.

A watannin Maris da Afrilu na 2012 yankin arewacin kasar ta Mali ya fada a hannun kungiyoyin jihadi da ke da alaka da Al-Qaida, wanda duk da korarsu da ka yi a watan Janairu na 2013 da sojojin kasar Faransa gami da na Majalisar Dinkin Duniya suka yi, har yanzu da sauran rina a kaba.