'Yan jihadi sun kame gidan Rediyo a Libiya
February 13, 2015Talla
Wasu hotuna da 'yan jihadin suka wallafa ta wani shafin Internet, sun nuno mutane dauke da makammai a cikin gidan radiyon bisa teburin da ake watsa shirye-shirye suna nuna bindigoginsu Kazalika su na saka kira'a ta Alkur'ani mai tsarki, da kuma jawabin shugaban 'yan jihadi na IS Abu Bakr Al-Baghdadi, da na kakakin kungiyar Abu Mohammed Al- Adnani a cewar mazauna ganin na Syrte.
Sai dai a cewar wani tsohon jagoran na birnin Syrte, har kawo yanzu dai ba'a ga wadannan 'yan jihadi suna yawo cikin garin ba, amma kuma sun fara ne da kame wannan gidan rediyo don su samu isar da sakonni ga al'ummar birnin. Birnin na Syrte dai, na mai zama mahaifar tsohon shugaban kasar ta Libiya marigayi Mouammar Kadhafi.