'Yan Ramadi sun kubuta daga hannun IS
December 24, 2015Rahotanni daga Iraki na cewa daruruwan mutane wadanda Kungiyar IS ta yi garkuwa da su a birnin Ramadi sun yi nasarar kubucewa tare ma da tserewa daga tsakiyar birnin a daidai lokacin da dakarun gwamnatin kasar ke ci gaba da dannawa a cikin birnin a wannan Alhamis.
Kakakin majalisar jihar Al-Anbar wacce birnin Ramadi ke karkashin ikonta ya ce daruruwan mutane akasarinsu yara kanana da mata da tsaffin wadanda mayakan Kungiyar ta IS suka yi garkuwa da su domin kare kansu daga harin dakarun gwamnatin kasar ne suka kubuce tare da tserewa daga tsakiyar birnin inda ake gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da mayakn Kungiyar ta IS.
Sai dai kuma ya ce tun a ranar Litinin mayakan Kungiyar ta IS sun kashe wasu iyalan da suka yi yunkuri tserewa.