1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda a Amurka sun kama shugaban hukumar IMF

May 15, 2011

Dominique Strauss-Kahn na cikin hanu 'yan sanda ana yi masa tambayoyi akan tuhumar da ake yi masa ta yin lallata da wata ma'aikaciyar Hotel

https://p.dw.com/p/11GJI
Dominique Strauss-Kahn Shugaban asusun IMFHoto: AP

Ana tsare da shugaban hukumar tsara kuɗaɗe na duniya IMF Dominique Strauss-Kahn a wani ofishin 'yan sanda da ke a birnin New York na Amurka inda ake yi masa tambayoyi.Ana zargin mista Strauss-Kahn da laifin yunƙuri yin lallata da kuma tsarewa na wata mata ma'aikaciyar' a wani Hotel inda ya sauka.

Straus kahn din ya na shirin tashin cikin jirgin sama ne zuwa birnin Paris lokacin da matar ta kai karan sa wajan yan' sanda. Wanda suka zabura suka fido shi daga cikin jirgin ,kafofin yaɗa labarai a Amurka na ta yaya ta wanan batu.Wani ɗan jarida ya ce wannan wani laifi ne mai tsanani da ya ka iya zama cikas ga Strauss Kanh akan aniyar sa ta siyasa.Kakkakin ´yan sandar New York Paul Brown ya shaidda cewa a cikin gauggawa ya bar salulansa da kuma wasu sauran kayyayaki a Hotel din.

Strauss Kahn wanda ake yi wa kallon ɗan takara a zaɓen shugaban ƙasa karƙashin tuttar jam'iyar socialiste ta `yan gurguzu na ƙasar Faransa a shekara ta 2012 .An shirya zai gana da shugabar gwamnatin jamus kafin wannan al'amari ya auku.Wannan kuma ba shi ne karo na farko ba da aka taɓa samun shi da irin wanan laifi ,ko a shekara ta 2008 sai da aka yi masa ahuwa akan laifin na yin lallata da wata ma'
aikaciyar asusun na IMF.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman