'Yan sanda da 'yan adawa sun gwabza a Kenya
October 3, 2017'Yan sanda a kasar Kenya sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa magoya bayan 'yan adawa da suka gudanar da zanga-zanga a birnin Nairobi babban birnin kasar ta Kenya bayan da madugun adawa Raila Odinga ya yi kira na a gudanar da zanga-zangar neman wasu jami'ai a hukumar zaben kasar su sauka daga mukaminsu.
Jami'an kungiyar agaji ta Red Cross sun fitar da wani jawabi da ya tabbatar da mutuwar wani mutum dan shekaru 41 a yankin Siaya da adawa ke da karfi a kasar ta Kenya.
Shi dai madugun adawa Odinga na zargin shugaban hukumar zaben mai zaman kanta da bada dama da ta jawo yin aringizo na kuri'u da suka ba wa Shugaba mai ci Uhuru Kenyatta dama ta ci gaba da darewa a kana karagar mulkin kasar.
Ya zuwa yanzu dai Kenyatta da Odinga ana kallon kallo yayin da ake shirin komawa akwatin zabe a cikin wannan wata na Oktoba don sake fafatawa a zaben na shugaban kasa.