SiyasaAfirka
Takun saka a siyasar Guinea Bissau
December 13, 2023Talla
'Yan sanda a birnin Bissau fadar gwamnatin kasar Guinea-Bissau sun watsa hayaki mai saka hawaye domin tarwatsa 'yan majalisa na bangaren adawa wadanda suka yi yunkurin haduwa duk da matakin Shugaba Umaro Sissoco Embalo na rusa majalisar.
A makon jiya shugaban kasar ya rusa majalisar wadda 'yan adawa suka mamaye, bayan wani yunkurin juyin mulki da aka yi inda aka samu harbe-harbe.
Karkashin dokokin kasar ta Guinea-Bissau da ke yankin yammacin Afirka, bangaren da yake da rinjaye a majslair dokoki yake nada jagororin gwamnati amma shugaban kasa yana da ikon rusa majalisar dokokin.