'Yan sandan Isra'ila sun kai samame ofis din Al Jazeera
May 5, 2024'Yan sandan Isra'ila sun kai samame Otal din da gidan talabijin din Al Jazeera ke amfani da shi a gabashin birnin Jerusalem a matsayin ofishinsa na yada shirye-shirye, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya tabbatar a Lahadin nan.
Karin bayani:Al Jazeera ta kai Isra'ila kotun ICC
Wani faifan bidiyo da ya karade shafukan Intanet, ya nuna jami'an tsaron cikin fararen kaya suna lalata naurorin daukar hoto na Al Jazeera a Otal din, biyo bayan umarnin majalisar ministocin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na haramtawa Al Jazeera yada shirye-shirye a kasar, sakamakon zargin zama barazana ga tsaron kasar.
Karin bayani:Zargin sojojin Isra'ila da kisan Shireen
Gidan talabijin din na Al Jazeera ya musanta zargin zama barazanar tsaro ga Isra'ila, yana mai cewar labari ne maras tushe balle makama, kuma wannan wani yunkuri ne kawai da Isra'ila ke yi wajen kara jefa rayuwar 'yan jarida cikin hatsari.
Kafar yada labaran Al Jazeera ta yi kaurin suna wajen sukar yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, kuma tana ci gaba da yada labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa game da yakin, ba dare da rana.