'Yan sandan Kenya sun binge mutum uku
November 17, 2017Talla
Kashe 'yan adawar uku na zuwa ne bayan da 'yan sanda suka ce suna yunkurin kwantar da zanga-zangar da magoya bayan Odinga ke yi, kamfanin dillancin labarun Faransa AFP ya ce, 'yan sanda sun fetsa ruwan zafi da hayaki mai sa hawaye kan ayarin madugun adawa, abin da ya hargitsa magoya bayansa yin martanin jifa da duwatsu kan jami'an 'yan sandan.
Kasar Kenya dai na cikin rudanin siyasa tun bayan da kotun koli ta soke sakamakon zagayen farko na zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Agusta, to sai dai da alamu tsugune bata kare ba, inda ake san ranar Litinin mai zuwa kotun koli za ta yanke hukunci kan ko za a rantsar da shugaba Uhuru Kenyata a mastayin shugaba karo na biyu ko za a sake zaben.