1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan Yuganda sun afka wa masu bore

August 20, 2018

'Yan sanda a Yuganda sun yi harbe-harbe a birnin Kampala a kokarin murkushe masu zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/33RUO
Uganda Proteste in Kampala
Hoto: picture-alliance/AP Photo/R. Kabuubi

Jami'an tsaro a Yuganda sun rufe wani bangare na Kampala babban birnin kasar tare da 'yan harbe-harbe gami da watsa hayaki mai sa hawaye, a kokarin tarwatse wani ayarin masu zanga-zanga a wannan Litinin, tare da kama akalla mutum 70.

Masu zanga-zangar na bore ne kan tsare wani dan majalisar dokoki kuma fitaccen mawakin nan wato Bobi Wine, wanda hukumomin ke ci gaba da yi tun ranar 13 ga wannan wata na Agusta.

An dai zargi dan siyasar ne tare da wasu mutum hudu da jifan ayarin motocin Shugaba Yoweri Museveni a yankin arewa maso yammacin kasar, lokacin wani gangamin yakin neman zabe.

Tsare Bobi Wine din wanda babban mai adawa ne da Shugaba Museveni, na ci gaba da tunzura jama'a da dama a Yugandar, inda ake ta kone-kone a wasu manyan titunin birnin na Kampala.