'Yan Saudi na son a shirya da Isra'ila - Pompeo
February 28, 2021Talla
Pompeo ya yi wadannan kalaman ne gabannin wani taro da aka shirya don yaki da kin jinin Yahudawa wanda a lokacin ne zai karbi wata lambar girma irinta ta farko da taron zai bayar a gobe Litinin idan Allah ya kaimu.
Baya kuma ga wasu 'yan Saudiyya da ya ce suna a daidaita da Isra'ilan, tsohon sakataren na harkokin wajen Amirkan ya ce wasu kasashe da dama ma na son daidata tsakaninsu da ita din sai dai bai bayyana sunayen kasashen ba.
Ya zuwa yanzu dai mahukuntan Saudiyya ba su mayar da martani kan wadannan kalamai na Pompeo ba.