Senegal: An tarbi 'an gasar AFCON
February 8, 2022Talla
Macky sall wanda ke yin jawabi a gaban dubban jama'ar da suka tarbi 'yan wasan na Lion na Senegal bayan fareti da aka yi da su a birnin Dakar ya ce suna cikin farin ciki.''Yau ga shi kun kai mu a matsayi na kololuwa na Afirka a wannan gasa, saboda bajimta da kuzari da ku ka nuna, dukkanin 'yan Senegal sun ji dadin wannan nasara. Wannan dai shi ne karon farko a tarihin kasar ta Senegal da ta ci kofin Afirka a cikin shekaru sama a 50 da soma yin gasar.