1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Siriya miliyan uku ne ke yin gudun hijira

August 29, 2014

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka yawan waɗanda rikicin Siriya ya raba da muhallansu ya kai kimanin miliyan uku.

https://p.dw.com/p/1D3sd
Irak Jesiden Flüchtlinge
Hoto: DW/R. Erlich

Shugaban hukumar Antonio Guterres ya ce wannan addadi da aka samu shi ne mafi yawa da aka taɓa gani a wannan zamani inda ya ƙara da cewar a shekarar da ta gabata kadai mutum miliyan guda ne suka tsere daga ƙasar sakamakon rikicin da ake yi.

Ƙaruwar yawan 'yan gudun hijirar na Siriya dai na zuwa daidai lokacin da 'yan ƙungiyar nan ta IS ke ci gaba da rajinsu na kafa daular Musuluci, lamarin da ya sa ake ganin yawan wanda za su kaurace wa ƙasar zai iya ƙaruwa nan gaba.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahamane Hassane