'Yan Sudan hudu sun mutu a zanga-zanga
June 9, 2019Talla
Rahotannin da ke fitowa daga Sudan na cewa jami'an tsaron kasar sun halaka akalla mutum hudu daga cikin masu zanga-zanga da yajin aikin gama gari a wannan Lahadi. Tun da fari dai jami'an 'yan sanda sun yi amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga- zanga da suka daddasa shingaye a kan titunan domin datse zirga- zirgar motoci.
Wani kwamitin likitoci da ke da alaka da masu boren ya tabbatar da mutuwar mutanen biyu a Khartoum, wasu biyun kuma a Omdurman. Kungiyoyin masu fafutukar samar da sauyi a Sudan sun lashi takobin ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnatin har sai an kafa gwamnatin farar hula da suke bukata.