'Yan Sudan na ci gaba da bore a Khartum
October 27, 2022Talla
Masu aiko da rahotanni sun ce an ga hayakin gurneti ya turnike arewacin babban birnin kasar Khartum a yayin da dubban masu boren suka kafa shingaye, a hankorinsu na neman ko ana ha maza ha mata a dawo da mulkin farar hula a kasar.
Tun bayan da Janar Abdel Fattah al-Burhane ya karbe mulki da tsinin bindiga daga wata gwamnatin farar hula, zanga-zangar adawa da salon mulkinsa ta karade wannan kasa, tare da zama silar mutuwar mutane da dama. Ko a unguwar al-Deim kadai da ke kudancin birnin Khartum da masu boren suka yi tattaki a wannan rana, an kashe akalla masu zanga-zanga 119 a cikin tsukin shekara guda.