Nijar: Hare-hare sun ritsa da farar hula
July 16, 2023Talla
A cikin wata sanarwa da rundunar ta bayyana, ta ce wasu yan taadda sun kai hari a kan wani rukunin jami'an jandarma na kasa a wani ayarin motocin rakiya a yankin Torodi-Makalondi. A cewar rahoton, mutane biyar suka mutu ciki har da wani jandarma da fararen hula hudu.Yayin da mutane 19 suka jikkata da suka hada da jandarmomi bakwai da sojoji biyar da fararen hula bakwai wadanda tuni aka kaisu asibitin a yamai. A bangaran yan ta'Aaddar kuma an kashe mutum biyu tare da kwace musu wasu makamai da babura guda biyu. Yankin na tilaberi da ke kan iyaka tsakanin Nijar da Burkina da Mali a kudu maso yammacin kasar, na yawan fuskantar hare-hare na 'yan ta'adda.