1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan taliban sun bayyana aniyar kissan pirsinonin Korea ta Kudu

August 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuF1

Dakarun gwamnatin ƙasar Afghanistan, sun watsa takardu ta sararin samaniya,a yankin Ghazni, inda yan taliban su ke ci gaba da garkuwa da wasu mutane 21 yan ƙasar Korea ta kudu.

A cewar mazauna yankin,Gwamnati ta fara hakan ne, da nufin kai hari a Ghazni,domin ceto pirsinonin da ƙarfin soja.

A yau ne saban wa´adin da ya taliban su ka baiwa gwamnati ya kai ƙarshen sa.

Kasancewar basu cimma biya bukata ba, sun bayyana aniyar ci gaba da da kissan wannan pirsinoni.

A cen ƙasar Korea ta kudu kuwa,yanmajalisar baki daya, sun bayyana wata sanarwa, inda su ka bukaci Amurika ta shiga tsakanin domin kawo ƙarshen wannan al´amari cikin ruwan sanhi.

Ministan harakokin wajen Korea ta Kudu, ya bayyana damuwa, ga matakin Afghanistan ba belin pirsinonin da ƙarfin soja.