'Yan Taliban sun kai jerin hare hare a Afghanistan
April 15, 2012'Yan bindiga a Afghanistan sun kai jerin hare hare masu alaka da juna a Kabul babban birnin kasar. 'Yan bindigar sun kai hari akan gine-ginen gwamnati da ofisoshin jakadanci na kasashen yamma da kuma sansanonin sojin NATO. Wani mai magana da yawun kungiyar Taliban Zabiullah Mujahid yace sune suka kai harin. Yana mai cewa mutanensu 'yan kunar bakin wake suka kaddamar da farmakin akan sojin NATO da ginin majalisar dokoki da kuma gidajen ma'aikatan diplomasiyya. Wuraren da harin ya shafa a birnin Kabul sun hada da ofishin jakadancin Amirka dana Birtaniya da kuma na Jamus. A wajen Kabul kuma 'yan bindigar sun kai hari gundumar Logar da filin saukar jiragen sama na Jalalabad da kuma ofishin 'yan sanda a garin Gardez dake lardin Paktya.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Usman Shehu Usman