1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Taliban sun kutsa cikin birnin Kunduz

Mouhamadou Awal BalarabeSeptember 28, 2015

Mayakan Taliban sun mamaye birnin Kunduz da ke Arewacin Afghanistan bayan mummunan fada tsakaninsu da dakarun gwamnatin wannan kasa.

https://p.dw.com/p/1GemF
Afghanistan Taliban Offensive bei Kundus
Hoto: picture alliance/AP Photo

Mayakan kungiyar Taliban sun yi nasarar kutsawa Kunduz da ke Arewacin kasar Afghanistan bayan da suka shafe lokacin suna fafatawa da dakarun gwamnati a kusurwowi uku na shiga wannan birni. Wadanda suka shaidar da lamarin sun bayyana cewar masu kaifin kishin addinin sun banka wa gine-gine da dama wuta ciki kuwa har da asibiti a hare-haren da suka kai da manya makamai.

Sai dai kuma Kakakin rundunar 'yan sanda na Kunduz Sayed Sarwar Hussaini ya nunar da cewar dakarun gwamnati sun kai wa 'yan Taliban farmaki da jiragen masu saukar ungulu, inda suka yi nasarar kashe 20 daga cikinsu. Ya kara da cewar sojojin gwamnatu uku na daga cikin wadanda suka jikata.

Wannan dai shi ne hari na biyu da Lardin Kunduz yake fuskanta a hare-hare daga 'yan Taliban cikin watanni uku da suka gabata.