1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Taliban za su tsagaita wuta a sallah

Mouhamadou Awal Balarabe MNA
June 9, 2018

Mayakan Taliban sun amince da shirin bude wuta a lokacin bukukuwan karamar sallah a Afghanistan kwanaki biyu bayan da shugaban kasa Ashraf Ghani ya dauki makamancin wannan mataki.

https://p.dw.com/p/2zCOg
Symbolbild Waffenstillstand mit den Taliban in Afghanistan
Hoto: picture alliance/Photoshot/J. Harper

Kungiyar Taliban ta sanar da shirin dakatar da fada da sojojin Afghanistan na tsawon kwanaki uku domin bai wa al'ummar Musulmi damar gudanar da bukukuwan sallar azumi cikin kwanciyar hankali. Wannan mataki ya kasance irinsa na farko da masu gwagwarmaya da makaman suka dauka cikin shekaru 17 da suka gabata, kuma ya zo ne kwanaki biyu bayan da shugaba Ashraf Ghani na Afghanistan ya sanar da shirin tsagaita bude wuta.

Sai dai kuma cikin sanarwar da suka bayar, 'yan Taliban sun bayyana cewa za su ci gaba da kai hare-hare a kan' yan kasashen waje a kasar, sannan kuma za su kare kansu idan an kai musu hari. Shirin tsagaita bude wutar zai fara aiki ne daga ranar karamar sallah ta Eid el-Fitr.

Idan za a iya tunawa dai, a ranar Alhamis da ta gabata, shi ma shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani  ya sanar da dakatar da bude wata daga ranar Talata mai zuwa da kungiyar Taliban, amma ya ce zai ci gaba da yakar kungiyar IS har sai ya ga abin da ya ture wa buzu nadi.