'Yan tawaye sun karbe kasar Syria inda shugaba Assad ya arce
December 8, 2024Da sanyin safiyar Lahadin nan aka fara ganin tabbacin alamun karshen mulkin iyalan gidan Assad na tsawon shekaru 50 a Syria, bayan da firaministan kasar Mohammed Ghazi Jalali ya sanar da cewa gwamnatinsu a shirye take ta mika wuya ga sabuwar gwamnati.
Mr Jalali ya bayyana hakan ne ta cikin wani jawabi da ya gabatar ta cin bidiyo da ya fitar, yana mai cewar yanzu yana gidansa bai gudu ba, to sai dai bai yi karin haske kan rahoton da ke cewa tuni shugaba Bashar Assad ya arce daga kasar ta filin jirgin saman birnin Damascus a Lahadin nan.
Karin bayani:Syria ta shiga mawuyacin hali na yaki da 'yan tawaye
Cikin daren Asabar 'yan tawayen HTS suka sanar da kwace birnin Hom, kuma a Lahadin nan suka kutsa cikin Damascus babban birnin kasar, tare da bude gidajen yari suna sakin daurarrun ciki, inda sojojin Bashar Assad suka tsere.
Karin bayani:'Yan tawayen Syria sun shiga birnin Aleppo
Tuni dai Amurka ta sanar da cewa shugaba Joe Biden na kallon al'amuran da ke faruwa yanzu haka a Syria, kamar yadda fadar White House ta sanar.