'Yan tawaye sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan ta Kudu
January 25, 2014Ministan yaɗa labaran Sudan ta Kudu ya ce ana ci gaba da tafka faɗa, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnati da 'yan tawaye.
Michael Makuei ya shaida wa manema labarai a birnin Juba cewa tun sa'o'i 24 bayan saka hannu kan yarjejeniyar ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye. Ya bayyana haka bayan dawowarsa da birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia inda aka saka hannu kan yarjejeniyar. Ministan ya zargi 'yan tawaye da karya yajejeniyar.
Amma tun farko 'yan tawaye sun zargi dakarun gwamnati da kai musu farmaki kan sansanonin da ke wasu jihohi biyu na tsakiyar kasar, zargin da gwamnati ta musanta.
A ranar Alhamis da ta gabata wakilan gwamnati da na tsohon mataimakin Shugaban kasa Riek Machar, suka saka hannu kan yarjejeniyar.
Kawo yanzu, rikicin mai nasaba da kabilanci ya yi sanadiyar hallaka dubban mutane cikin kasar ta Sudan ta Kudu, yayin da wasu fiye da rabin milyan suka tsere daga gidajensu.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinaɗo Abdu Waba