'Yan tawaye sun saki 'yan kasashen waje
April 1, 2017Talla
Mayakan tawayen kasar Sudan ta Kudu, sun sanar da sakin wasu ma'aikatan kamfanin mai 3 da suka yi garkuwa da su a farkon wannan watan.
Jagoran 'yan tawayen kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar ne dai ya bayar da umurnin sakin ma'aikatan man, kamar yadda kungiyar SPLA ta sanar.
Ma'aikatan kamfanin man dai 'yan asalin kasashen Pakistan ne da kuma India.
Tuni kuma aka fire da su zuwa birnin Khartoum na kasar Sudan, kamar yadda ministan harkokin wajen Sudan ya tabbatar.