1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan tawayen Abzinawa na amfani da jiragen yakin Ukraine

October 15, 2024

Ukraine ta musanta zargin bai wa 'yan tawayen Abzinawan Mali tallafin jirage marasa matuka domin yakar dakarun gwamnati.

https://p.dw.com/p/4lpJc
Wani jirgi marasa matuki da ke shawagi a yankin Gao na Mali a shekarar 2016.
Wani jirgi marasa matuki da ke shawagi a yankin Gao na Mali a shekarar 2016.Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Jaridar Faransa ta Le Monde ita ce ta wallafa labarin da ke cewa 'yan tawayen na Abzinawa da ke gwagwarmaya da makamai na amfani da jirage marasa matuka na Ukraine domin kai hare-hare a wasu sassan Mali, kamar yadda suma sojojin Malin ke samun goyon bayan daga sojojin hayan kamfanin Wagner na Rasha.

Karin bayani: Rasha ta kakkabo jiragen Ukraine marasa matuka

Ministan Harkokin Wajen Ukraine ya musanta zargin da jaridar Le Monde ta wallafa na ba wa 'yan tawayen jirage marasa matuka samfurin UAV. A watan Augutan 2024, Mali ta yanke huldar diflomasiyya da Ukraine bisa zargin tallafawa 'yan tawayen da makamai wanda ya kai su ga halaka sojojin Mali da dama da kuma wasu sojojin hayan Rasha na Wagner a yankin arewacin Mali.