Yanayin da masu bukata ta musamman ke rayuwa a birnin Maradi
December 3, 2024Jamhuriyar Nijar ta sha rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama da ke kare hakkin dan Adam, ciki har da ta kare hakkin masu bukata ta musaman. Wannan dalili ne ya sa ta daukar dokar da ta yi umurnin kula da hakkin masu nakasa a gine- gine na gwamnati da na masu zaman kansu, don ba su damar shiga da fita da kai kawo cikin sauki ta la'akari da halin da suke ciki. Sai dai har yanzu da sauran jan aiki saboda kalilan daga cikin gine-ginen ne suka yi la'akari da hakkin masu bukata ta masumman, kamar yadda Yahaya Ousman, shugaban hadakar kungiyoyin masu bukata ta musaman na jihar Maradi ya bayyana.
Karin bayani: Kere-keren masu bukata ta musamman a Kaduna
Gwamnatin Nijar da Kungiyoyin kasa da kasa sun dade suna fafutukar ingata rayuwar masu bukata ta musaman a Nijar, amma duk da haka da sauran rina a kaba musaman a fannin gine-gine, a cewar Ramma Abdou, shugabar mata masu bukata ta musaman ta jihar Maradi. Shi kuwa Abdoulaye Ousman Abdou mai dauke da larurar rashin gani, kuma malamin makarantar masu larurar gani, ya ce gine-ginen baya-bayanan nan musaman na makarantun boko sun fara aiki da wannan doka.
Karin bayani: Bikin ranar masu bukata ta musamman a Njiar
Kungiyoyin kare hakki dan Adam irin su ANDDH na aiki kafada-kafada da kungiyoyin masu bukata ta musamman wajen sa ido matuka gaya don ganin mahukanta sun matsa kaimi wajen samar da gine-gine masu la'akari da hakkokinsu kamar yadda doka ta yi tanadi, kamar yadda Sadissou Abdou shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam na birnin Maradi ya bayyana. A game da maatsaloli kuwa, ko a baya-bayan nan shugabanin kungiyarsu ta kasar NIjar ta gana da firaminista don sanar da shi halin da suke a ciki. Amma ana jiran ganin matakan da hukumomin mulkin soja za su dauka dan ganin an fidda hakkin masu bukata ta musamman a gine-ginen ma'aikatun gwamnatin Nijar