1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yanayin zaɓen Tanzaniya

November 1, 2010

A ƙasar Tanzaniya an bayyana zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisa da ya gudana, a matsayin wanda aka yi cikin lumana

https://p.dw.com/p/Pvrg
Shugaban Tanzaniya Jakaya KikweteHoto: DW

A karon farko tun shekaru 50 bayan samun yancin kai, jam'iyar CCM dake mulki a ƙasar Tanzaniya ta fara jin tsoron rasa rinjayen da take da shi a harkokin mulkin ƙasar. Da farko dai a gabanin zaɓen ƙasar, ƙuri'ar jin ra'ayi ta nuna cewa jam'iyarce zata samu gagarumin rinjaye amma bayan zaɓen sai aka ga duk da nasarar da ta samu amma bai kai yadda aka zata ba.

Ga yadda akaka bada rohotonni kama daga lokacin zaɓe da bada sakamako, za'a iya cewa komai ya tafi ba tare da tashin hankali ba, kuma ko da masu lura da zaɓen sun bada shaidar hakan. To amma ita ma kanta gwamnati, ta fara shakka abokan adawa musamman daga jam'iyar Chadema, wandake da rajin inganta demokardiyya da tattalin arziki. Abdurraham Kinana shine daraktan yaƙin neman zaɓe na shugaba mai ci.

"Yace dama abune da aka za ta, za'a samu gogayya. Amma dai zan iya cewa zaɓe ya gudana cikin ruwan sanyi. Abun farin ciki shine muna da yaƙinin jam'iyar mu za ta samu rinjaye a majalisar dokoki, kuma tabbacin hakan ya bayyana, sabo da ɗan takaranmu a shugabancin ƙasa shine ya samu rin jaye kan sauran 'yan takara"

Ita kuwa jam'iyar adawa ta Chamenda wanda ke bin bayan ta shugaban ƙasa, ta sanar da cewa ko ba komai sunyi rawar gani a wannan zaɓen domin hukumomi dake mulki basu zaci lamarin zai kasance musu mai wuya kamar haka ba. Sai dai daraktan yaƙin neman zaɓe na jam'iyar ta Chamenda Mwesigu Baregu yace wani abinda za su buƙaci a kawo sauyi nan gaba, shine tsawon kwanakin yaƙin neman zaɓe.

"Wani abinda zan iya cewa na lura da shi, shine bayan tsawon kwanaki 67 muna yaƙin neman zaɓe, wannan wani matakine mai tsawo, shin ko muna buƙatar lokaci mai tsawo kamar wannan, domin akwai gajiyarwa. Ina fatan za mu sake tattauna wannan lamarin, shin ko akwai wata ma'ana ta ɗaukar tsawon lokaci muna yaƙin neman zaɓe"

Su ma kansu ƙungiyoyin sa'ido sun yaba da yadda zaɓen na ƙasar Tanzaniya ya gudana, kamar yadda Yvonne Kilonzo ɗaya daga cikin jami'an sa'ido daga ƙungiyar Tarrayar Afirka ta shaidawa manema labarai.

"An yi shi cikin lumana, babu wani dodorido. Babu matsalar da muka lura da ita, wanda za ta damu wani, komai ya tafi dai-dai. Akwai wasu wurare biyu da muka samu masu kaɗa ƙuri'a sun zo ba su ga sunayensu ba, amma dai waɗannan wuraren ma suna nesa da juna. Amma dai a wuraren da ni da kaina na ziyar ta, komai ya tafi dai-dai matuƙa"

A gabanin hukumar zaɓe ta fidda sakamakon zaɓen baki ɗayansa dai, ko wa yana saran cewa shugaba Jakaya kikwete ne zai lashe zaɓen, to amma ba zai samu yawan rinjayen da ya samu shekaru biya na baya ba.

Rohotonni daga tsibirin Zanzibar dake wani ɓangaren ƙasar ta Tanzaniya, shima ya nuna cewa ɗan takaran jam'iya mai mulki wato Chama Cha Mupindazi ita ce ke kan gaba. Sai dai a tsibrin na zanzibar anfi samun gagayya tsakanin yan dawa da masu mulki, inda wasu matasa kimanin 500 suka kewaya hukumar zaɓen ƙasar, suna neman sai a gaggauta sanar da sakamakon zaɓen ƙasar. An dai tura yan sandan kwantar da tarzuma a ofishin hukumar zaɓen dake tsibirin Zanzibar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu