'Yar Kenya ta samun lambar yabo ta Jamus
April 4, 2019An zabi matar wacce kwararriya ce a fannin ilimin konfuta da kimiyar sadarwa ta yanar gizo daga cikin mutane 18. Rotich ta lashe wannan kyauta ce a sakamakon rawar da ta taka wajen kawo sauyi da kirkire-kirkiren sabbin manahajojin sadarwa ta yanar gizo da suka hada da manahajar da ta kira Ushahidi da ta kirkiro a shekara ta 2007 wacce ta taimakawa wajen samun labarai masu yawa daga kasar Kenya wacce kuma aka yi amfani da ita a kasashe sama da 160 domin shawo kan rigingimu da kuma sa ido ga zabuka a kasashe kamar su Najeriya da Afganistan da ma a lokacin afkuwar bala'i a kasashen Chili da Haiti da New Zeland.
Kazalika Rotich ta kirkiro da wata na'urar sadarwa ta yanar gizo ta zamani mai aiki da batir da ke iya share awoyi shida tana aiki ba tare da bukatar caji ba, na'urar da yanzu haka ake aiki da ita a kasashen 150 na duniya.
A shekara ta 1993 ne dai gidauniyar German Afrika Foundation ta kirkiro da wannan kyauta ga 'yan Afirka dake taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya, da kare hakkin dan Adam da kuma inganta harakokin tattalin arziki da kyautata rayuwar dan Adam a Nahiyar.
Da take jawabi bayan samun wannan kyauta Rotich ta ce ta yi imanin bunkasa kamfanonin sadarwa ta yanar gizo da da ma matsakaita da kananan kamfanoni zai iya yin tasiri ga habbakar tattalin arzikin kasarta