1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara miliyan 230 ke rayuwa cikin kunci a duniya

Sabine Kinkartz/ Muohamadou Awal BalarabeJuly 1, 2015

Asusun kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF a sabon rahotonta. cewa ta yi samar da ilimin, kula da lafiyar da karesu daga cin zarafi sun zama alkawuran da ba a cikawa a kasashen da ke fama da rikice-rkice.

https://p.dw.com/p/1FrRK
Afrika Bildergalerie Kindersoldaten im Süd-Sudan
Hoto: DW/A. Stahl

Asusun ya nunar da cewar Hasali ma dai a kasashen biyar da suka hada da Siriya, Sudan, Iraki, Yamen, Sudan ta Kudu da kuma Jamuriyar Afirka ta Tsakiya, yara miliyan 21 ne ke rayuwa cikin mawuyacin hali sakamakon yake-yake. UNICEF ta daura alhaki a kan kungiyoyin tarzoma kamar su IS a yankin Gabas ta Tsakiya da Boko Haram a yankin yammacin Afirka, saboda watsi da suke yi da dokokin kasa da kasa a kan hakkin yara, domin cimma manufofinsu na jan hankalin duniya. Ko da shi ma Ted Chaiban babban jami'in UNICEF sai da ya yi tir da abin da ke faruwa a fagen yaki.

"A bara yake-yake sun jefa miliyoyin yara da iyaye a cikin mawuyacin hali. An ta harbawa yara bama-bamai a kan gadajensu da ma dai makarantunsu. A wani bangaren ma an yi garkuwa da su, ko kashesu tare da sanyansu aikin soji ba da son ransu ba."

Asusun UNICEF ta ce ko wane yaro guda daga cikin 10 a fadin duniya, na tasowa ne a yankuna da ake fama da yaki, ko wasu nau'o'i na tashe-tashen hankula. Rabon a samu yara a halin tagayyara irin wannan tun zamanin yakin duniya na biyu. Saboda haka ne Asusun ya bukaci tallafin makudan kudade domin dawainiyar yara a kasashen da ake yake-yake. A bana kawai, UNICEF na bukatar miliyan dubu uku na Dollar Amirka, domin gudanar da wannan aiki. Sai dai kuma ta na fuskantar matsala wajen samun kudi, alhali kashi biyu bisa uku na kudin na fitowa ne daga kasashen mambobi, ya yin da daya kason kuwa ke zuwa daga kungiyoyi masu zaman kansu.

Shugaban Reshen UNICEF a kasar Jamus Jürgen Heraeus ya yi tsaokaci a kan batu ya na mai cewar:

"Tallafi ya fi saukin samuwa inda bala'i daga indallahi ya afku fiye da wanda ake bukata don kulawa da 'yan gudun hijirar Siriya ga misali. Mutane na nunar da cewa wani bal'i ne da su ma zai iya samunsu, ma'ana suna tausayawa. Amma kuma game da sauran rikice-rikicen cewa suka yi bai shafeni ba."

A shekarun baya-bayannan dai, yara dubu 70 ne aka haifa a sansanonin 'yan gudun hijira a duniya. Sai dai kuma ministan raya kasashe na Jamus Gerd Müller ya ce abin takaicin shi ne rashin kula da su yadda ya dace.

"Tsarin samar da abinci na duniya da kuma UNICEF sun rage yawan abinci da suka saba baiwa yara a kowace rana, sakamakon karancin kudi. Saboda haka yara da sauran matasa za su shiga cikin wani mawuyacin hali sakamakon rashin tallafi."

Ita dai ma'aikatar raya kasa ta Jamus ta taimaka wa UNICEF da kudi miliyan 150 a bara, domin ta yi dawainiyar yara a kasashen da ake fama da rikice-rikice. An yi amfani da wani kaso na wannan kudi wajen kula da karatu da kuma lafiyar, yaran da yaki ya sa su kauracewa matsugunansu a kasashen Syriya da kuma Iraki.

UN Millenniumsziele Schule in Afghanistan
Hoto: UN Photo/Shehzad Noorani
Symbolbild Kindersoldaten
Hoto: picture-alliance/dpa/A.Ufumeli