Cutar tamowa na barazana ga yaran Habasha
August 10, 2021Talla
UNICEF ta baiyana damuwarta kan barazanar yunwa da yara kanana ke fuskanta a kasar Habasha, yara kimanin miliyan hudu ne za su fuskanci tsananin yunwa a sakamakon kazancewar fada a yankin Afar da Tigray, ta nemi bangarorin biyu, da su dakatar da fadan don ceto rayukan wadannan yaran.
Daga cikin wasu sama da dubu dari hudu da rikici ya raba da muhallansu, akwai yara da dama da iyayensu suka yi gudun hijira da su, da ke fama da cutar tamowa inji Unicef.