Neman dauki ga yaran Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
November 30, 2018Talla
Tun da yaki ya barke a 2013 fiye da mutane miliyan daya ne suka guje wa muhallansu yayin da kusan miliyan uku daga kusan miliyan biyar ke cikin tsanani na bukata. A cewar Asusun UNICEF muddin al'umma ba su koma gonakinsu ba, babu makawa a shekaru masu zuwa za a fuskanci babbar matsala ta yunwa a wannan kasa.
A cewar rahoton fadakarwar na Majalisar Dinkin Duniya kan halin da yara kananan ke ciki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wacce yakin da take ciki bai samun kulawar da ta dace, kimanin yara dubu 43 da ke kasa da shekaru biyar za su samu kai a yanayi na fuskantar barazanar mutuwa saboda rashin abinci mai gina jiki a shekarar 2019. Rashin abincin dai na zame masu sila ta saurin samun cututtuka kamar maleriya da kyanda ko ma amai da gudawa.