Yara 'yan gudun hijira
Yara da dama maza da mata da ke tsere wa yaki ko fatara da ake fama da shi a kasashensu daga yankin Asiya da Afirka da Gabas ta Tsakiya ke cikin dinbim mutane da ke kasadar biyo wa ta teku domin zuwa nahiyar Turai.
Rashin tabbatacciyar makoma
Dubban Yazidawa ke gudun aiyyukan ta'addancin kungiyar IS tun daga shekarar da ta gabata, babu wanda ya san sanda za su koma kauyukansu cikin tsaunikan Sinjar kamar wannan yaro da ke sansanin 'yan gudun hijira na Silopi kusa da iyakar Iraki da Turkiya, har yanzu ba su da tabbaci kan makomarsu.
Samar da gadaje a sansanin 'yan gudun hijira
A yawancin biranen Jamus, mutanen da ke neman muhalli ana sama musu na wucin gadi cikin katafaren gini, a wannan wurin wasanni a Arewacin Bavaria garin Neustadt bei Coburg karamin yaro ne ke taimakawa a hada gadaje dan kwanciya da daddare.
A yankin da ba mai iko da shi
Ko da yake wannan yarinya ta tsinci kai cikin rashin ina ta nufa a tsakanin Girka da Masedoniya fuskarta na cike da murmushi babu karaya a tare da ita, makonni kadan da suka gabata dubban mutane sun tsallaka yankin dan samun jirgi zuwa Sabiya daga nan su karasa kasar Hangari.
Bacci a tsakanin hanya cikin jirgi
Cikin jirgi makare da jama'a a kan hanyarsa daga birnin Budapest zuwa Munich 'ya'yan 'yan gudun hijira ne ke kwance a kan hanya da aka tanada tsakani dan wucewa cikin jirgi, Kamar sauran dubban 'yan uwansu suna son zuwa Yammacin Turai bayan ratsa yankin Balkan. Kasar Hungari kamar takwarorinta na EU ta bari sun ratsa kasar kafin daga bisani ta rufe iyakarta.
Guje wa yakin basasa
A kasar Yemen dubban mutane ne ke tattara iyalansu da abin da suka mallakadan kaurace wa tashin hankali a wannan kasa da ke zama matalauciya a tsakanin kasashen Larabawa. Mayakan Houthis 'yan tawaye na ci gaba da fafata fada da dakarun sojan gwamnati da ke samun goyon bayan sojan Saudiyya, cikin dubbai wadanda suka rasu a yakin da ya dauki watanni da yawa kananan yara ne.
Hawa layi dan samun abinci
Ba tare da samun tallafin kasashen waje ba mutane da dama a Siriya da sun mutu. Wadannan yara na hakuri su bi layi dan samun abinci a sansaninsu da aka kafa a Idlib.
Sabon tsarin sufuri
Yadda za a sayi tikitin jirgi dan zirga-zirga a sabbin yankunan da 'yan gudun hijira suka samu kansu, na daya daga cikin abubuwan da bako zai koya da zuwa Jamus. A nan ministan sufuri a jihar Saxony-Anhalt, Thomas Webel, na ba wa yara darasi kan yadda ake amfani da na'urar siyan tikiti.
A wajen sansanin 'yan gudun hijira
Kungiyar da ke lura da 'yan gudun hijira ta kasa da kasa ta ce fiye da mutane 121,000 ne suka tsallaka tekun Bahar Rum daga Afirka zuwa Italiya cikin jiragen ruwa marasa inganci, fiye da 2,600 kuma sun rasu a kokarinsu na tsallakawa, mafi akasarinsu na son nausawa ne Arewaci. Ga wannan yaron da iyayensa sansani da suka tsaya a tsibirin Lampedusa wata kila na iya zama tasha ce kawai ta wucin gadi.
Makaranta a matsayin abar dauke kewa
Zuwa makaranta na dauke hankali kan damuwar da ake samu a rayuwar yau da kullum a sansanin 'yan gudun hijira na Thet Kel Pyin a Myanmar. Dubun-dubatar 'yan kabilar Rohingya da ke zama Musulmi ne marasa rinjaye da aka rabasu da kauyikansu, sun yi kaura zuwa wasu yankuna a Kudu maso Gabashin Asiya ko wasu kasashen na waje.
Rayuwar yarinta ta koma ta soji
A kasashen Afirka da a ke fama da tashin hankali yara kanana ana tilasta musu shiga aikin soji. Da wahala a ga yara ko wadanda suka shiga shekarun balaga su tsira daga fadawa cikin kungiyoyin 'yan tawaye kamar yadda yake a nan jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Kaurace wa muhallai saboda Boko Haram
Kungiyar Boko Haram ta 'yan ta'adda ta sanya tsoro da fargaba a zukatan al'umma a Arewacin Najeriya da makwabtan kasar. Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa kimanin yara miliyan daya da dubu dari hudu ne suka bar mahallansu saboda Boko Haram. A nan yara ne ke samun kalaci a cibiyar rijistar 'yan gudun hijira a Geidam a Arewacin Najeriya.