Yarjejeniya tsakanin EU da Brazil
July 5, 2007Ƙungiyar gamayya turai da Brazil, sun cimma yarjejeniya a game da ƙulla mu´amila ta mussaman tsakanin su.
A wannan taron farko da ya haɗa ɓangrorin 2 a birnin Lisbonne na ƙasar Portugal, sun yanke shawara ƙarfafa cude ni cude k ata fannoni da dama da su ka shadfi saye da sayarwa siyasa da kuma dioploamatia.
A taron manema labarain haɗin gwiwa shugaban ƙungiyar gamayya turai bugu da ƙari, Praminstan Portugal Jose Socrates, ya dangata yarjejeniyar da wata babba nasara da Portugal ta cimma, a yaunin da aka ɗora mata na shugabacin ƙungiyar EU.
A nasa ɓangare shugaban hukumar zartaswa na EU Jose Manuel Baroso, ya ce a halin yanzu an shiga saban tafarki mai inganci tsakanin Turai da Brazil.
Shugaban ƙasar Brazil Luiz Inacio Lula da Sylva, ya yi anfani da wannan dama, inda ya buƙaci ƙasashen turai su maida himma, wajen cimma yarjejeniya a tanttanawar da ta cije, a ƙungiyar cinikya ta dunia.