1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniya tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

September 27, 2012

Sulhun da aka cimma tsakanin El-Beshir da Salva Kiir bai warware muhimmiyar taƙƙadama tsakanin ƙasashen biyu ba.

https://p.dw.com/p/16GS7
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugabanin ƙasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun cimma wata 'yar ƙwarya-ƙwaryar yarjejeniyar bayan kwanaki ukku na tattanawa a birnin Adis- Ababa na ƙasar Ethiopiya.

Tun bayan da Sudan ta Kudu ta sami 'yancin kanta a shekara da ta gabata,a ka shiga takon saƙo tsakanin ta da Sudan.A watani Maris da Mayu na wannan shekara saida ma dakarun ƙasashen biyu su ka ba hammata isaka, kamin daga bisani su tsagaita wuta.

Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyar Tarayya Afrika sun yi kira ga hukumoin Khartum da na Juba su koma tebrin shawara domin warware rikicin da ke tsakaninsu cikin ruwan sanhi.

Ranar 22 ga wannan wata wa'adin da gamayyara ƙasa da ƙasa ta ba su cika.

Leader of the Sudan People's Liberation Movement (SPLM), Salva Kiir Mayardit (L) chats with Sudanese President Omar al-Bashir (R) during the swearing-in ceremony in Khartoum, Thursday 11 August 2005. Salva Kiir was sworn in as the country's senior vice president Thursday, taking over after his predecessor John Garang died in a helicopter crash. EPA/PHILLIP DHIL - BEST QUALITY AVAILABLE +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa/dpaweb

Bayan kwanaki hudu na tattanawa, shugaba Omar Hassan Al-Beshir da takwaransa Salva Kiir na Sudan ta Kudu, sun cimma daidaito akan wasu daga cikin matsalolin, to amma cewar Karl Wohlmuth ƙurrare game da Sudan a jami'ar birnin Bremen da ke nan Jamus, har yanzu ba a rabu da Bukar ba:

"Matsalolin da suka fi sarƙƙaƙiya sune na shata iyakoki,domin akwai yankunan da ƙasashen biyu kowa ke iƙirarin mallakarsa ne.Ko da an cimma yarjejeniya,muddun ba a mangace wannan matsala ba,to za a komawa gidan jiya noman goje,ƙasashen biyu za su ɗauki lokaci mai tsawo kamin su cimma masalaha."

Wasu daga matsalolin da ƙasashen biyu ke rikicin kansu, sun haɗa da mallakar yankin Abyie mai arzikin man fetur.

A tunanin Wolf-Christian Paes shima wani masani game da Sudan a cibiyar nazarin al'amuran ƙasa da ƙasa dake birnin Bonn har yanzu da sauran tafiya game da batun warware rikicin Sudan da Sudan ta Kudu:

"Ayoyin tambaya dake tattare da wannan yarjejeniya sune shin ƙasashen biyu sun yi ta ne da zuciya guda, koko dai kawai dole ce ƙaunar naƙi, domin su ƙubuta daga takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi barazanar kargama masu idan ba su cimma masalaha ba?A ƙashin gaskiya matsaloli na zarhiri wanda ƙasashen biyu ke jayyaya kan su har yanzu sunan nan ba a warware su ba, saboda haka, da alamu nan da 'yan watani shida ciwo ya koma ɗanye".

A cewar Karl Wohmuth, idan ana san magance wannan matsa dindin , cilas sai an haɗa batun siyasa da na tattalin arziki, ta hanyar raya yankun dake kan iyakokin ƙasashen biyu:

" Matakin da zai taimaka a samu zaman lafiya mai ɗorewa shine, ƙaddamar da tsarin mai ƙwari na taimakawa jihohi biyar na kan iyakoki daga ko wane ɓangare.Duk wani yunƙurin da za a yi, ba zai tasiri ba,muddun ba a ɗauki wannan mataki ba".

--- DW-Grafik: Per Sander 2011_02_08_sudan_südsudan.psd

Hausawa kan ce wanda zai sama idan ya taka fafifai ya cigaba, saboda haka ko ba ma komai, hawa tebrin shawara tsakanin shugaba Omar Hasan El Beshi da Salva Kiir na matsayin wata nasara a ƙoƙarin samun zaman lafiya mai ɗorewa tsakanin wannan ƙasashe masu gaba da juna.

Mawallafa:Ludger Schadomsky/ Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu