EU da Nija za su dakile safarar bil'Adama
July 16, 2022Talla
Kungiyar Tarayyar Turai da Jamhuriyar Nijar na shirin hada karfi da karfe don yakar safarar bil'Adama da ke addabar nahiyoyin biyu.
Hukumar EU ta ce yarjejeniyar yaki da safarar bakin haure da ta kulla da Jamhuriyar Nijar ka iya taimakawa matuka wajen kakkabe 'yan baranda masu mummunar tabi'ar nan ta safarar bani Adama da jigilar bakin haure zuwa nahiyar Turai.
Tun da jimawa Jamhuriyar ta Nijar ke zama wata hanya tilo ta kwararar bakin haure daga kasashen yankin yammacin Afirka da dama, wadanda ke shiga Libiya da zummar zuwa Turai ta barauniyar hanya.